'Yan Rasha sama da dubu 40 sun kamu da cutar corona a kwanaki 4
Wallafawa ranar:
Ga dukkanin kasar Rasha ta kama hanyar zama sabuwar cibiya ta annobar coronavirus ko COVID-19, la’akari da yadda dubban ‘yan da sauran mazaunanta ke kamuwa da cutar a kowace rana.
Hukumomin lafiya a Yau laraba sun ce karin sabbin mutane dubu 10 da 559 gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus a rana 1.
Karin adadin na sama da mutane dubu 10, ya sanya karuwar yawan jumillar wadanda annobar ta kama a kasar ta Rasha kaiwa dubu 165 da 929, daga cikinsu kuma dubu 1 da 537 sun mutu.
Yanzu haka Rasha ta koma kasa ta biyar a Nahiyar Turai da annobar COVID-19 tafi yiwa ta’adi, bayan Spain, Italiya, Birtaniya da kuma Faransa.
Alkalumman hukumomin lafiya sun nuna cewar, tun daga ranar lahadi 3 ga watan Mayu na wannan shekara, mutane sama da dubu 10 ke kamuwa da cutar ta coronavirus a kowace rana.
Sai dai duk da karuwar adadin masu kamuwa da cutar, har yanzu annobar ba ta soma tafka barnar halaka dubban mutane ko daruruwa ba kowace rana a Rashan, kamar yadda aka gani a kasashen da ke yankin yammacin Turai, irinsu Italiya, Spain, Birtaniya da kuma Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu