Diflomasiya

Venezuela ce za ta hukunta Amurkawan da suka so yi min juyin mulki - Maduro

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro. REUTERS/Manaure Quintero

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro yace za’a yiwa Amurkawa biyu da aka kama da hannu wajen yunkurin kifar da gwamnatinsa shari’a a cikin kasar, bayan jami’an tsaro sun dakile yunkurin a karshen mako.

Talla

Maduro ya bayyana Amurkawan a matsayin wadanda suka amsa aikata laifukansu, bayan an kama su dumu dumu, kuma yanzu haka babban lauyan gwamnati ya dauki mataki akansu.

Sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace za su yi amfani da duk hanyar da ta dace wajen kubutar da Amurkawan.

A nata bangare Rasha tace hujjar da Amurka ta gabatar na rashin hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Venezuelan ba abu ne mai gamsarwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI