Coronavirus-Amurka

Coronavirus ta raba karin Amurkawa miliyan 3.2 da ayyukansu

Wasu Amurkawa tsaye a gaban wani ginin gwamnati suna jiran samun hakkokinsu na barin aiki, Las Vegas dake Nevada a Amurka. 17/3/2020.
Wasu Amurkawa tsaye a gaban wani ginin gwamnati suna jiran samun hakkokinsu na barin aiki, Las Vegas dake Nevada a Amurka. 17/3/2020. AP Photo

Gwamnatin Amurka tace wasu karin mutane miliyan 3 da dubu 200,000 sun sake gabatar da kansu domin samun tallafi, sakamakon rasa gurabun ayyukan yi sakamakon illar da annobar coronavirus ta yiwa kasar.

Talla

Alkaluman da ma’aikatar kwadagon kasar ta gabatar sun nuna cewar wadanan sabbin alkaluma ya tabbatar da cewar mutane sama da miliyan 33 da rabi suka rasa aikin yi a fadin Amurka.

A karshen watan Afrilu, gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa, adadin wadanda da suka rasa ayyukanyi a kasar ya zarce miliyan 30, sakamakon yadda annobar coronavirus ke cigaba da yin tasiri wajen durkusar da tattalin arzikin kasashen duniya ciki harda na Amurka.

Tarihi ya nuna cewar jimillar wadanda suka rasa ayyukan nasu a Amurkan shi ne adadi mafi yawa da kasar ta taba gani tun shekarar 1930.

Ya zuwa yanzu annobar COVID-19 ta kashe mutane dubu 73 da 95 a Amurka bayan ta kama mutane miliyan 1 da dubu 227 da 430.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.