Rasha-Coronavirus

Karin 'yan Rasha sama da dubu 11 sun kamu da cutar corona a rana 1

Wasu jami'an kiwon lafiya a Rasha yayin binne mutanen da annobar coronavirus ta kashe a wata makabarta dake wajen birnin Saint Petersburg. 6/5/2020.
Wasu jami'an kiwon lafiya a Rasha yayin binne mutanen da annobar coronavirus ta kashe a wata makabarta dake wajen birnin Saint Petersburg. 6/5/2020. OLGA MALTSEVA / AFP

Kasar Rasha ta sake gabatar da adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da annobar COVID-19 a yau alhamis, wadanda suka zarta sama da 11,000.

Talla

Alkaluman da hukuma suka gabatar sun nuna cewar an samu sabbin mutane 11,231 da suka kamu da cutar a cikin sa’oi 24, abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa 177,160.

Yanzu haka dai hukumomin Moscow, babban birnin kasar ta Rasha ya sanya dokar hana fita sakamakon yadda yawan masu kamuwa da cutar ta coronavirus ke hauhawa a kowace rana.

Kasar Rasha a yanzu ta koma kasa ta 4 a jerin kasashen da aka fi samun masu dauke da cutar a Turai kuma itace ta biyar a duniya.

Alkalumman hukumomin lafiya sun nuna cewar, tun daga ranar lahadi 3 ga watan Mayu na wannan shekara, sama da mutane dubu 10 ke kamuwa da cutar ta coronavirus kowace rana a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.