Turai na bikin cika shekaru 75 da kawo karshen Yakin Duniya na 2

Wasu dubban sojin Amurka yayin fareti a Champs Elysees dake Paris a Faransa, kwanaki 4 bayan kwato birnin daga mamayar sojojin Nazi a ranar 29 ga Agustan 1944.
Wasu dubban sojin Amurka yayin fareti a Champs Elysees dake Paris a Faransa, kwanaki 4 bayan kwato birnin daga mamayar sojojin Nazi a ranar 29 ga Agustan 1944. Peter J. Carroll / AP

Nahiyar Turai na bikin cika shekaru 75 da kawo karshen yakin duniya na biyu, yayinda annobar COVID-19 ta sanya soke bukukuwan da aka shirya gudanarwa domin tuna ranar.

Talla

Ana sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier za su ajiye furanni a wajen bikin tuna wadanda suka mutu, yayin da birnin Berlin ya bada hutu ga ma’aikata domin karrama mutane sama da miliyan 50 da suka mutu a yakin, a nahiyar Turai.

Shugaban Jam’iyyar 'yan ra’ayin rikau Alexander Gauland yayi watsi da shirin gudanar da bikin, inda ya bayyana ranar a matsayin ranar da aka samu nasara kan Jamus.

A baya kasar Rasha ta shirya gudanar da kasaitaccen biki domin tuna ranar a gobe asabar, wanda aka tsara shugabanin kasashen duniya za su halarta cikinsu harda shugaba Faransa Emmanuel Macron, a dandalin 'Red Square' amma annobar COVID-19 ta sanya soke bukukuwan.

Sai dai ana sa ran shugaba Vladimir Putin ya ajiye furanni a gaban mutuum mutumin da ake girmama sojin da suka wakilci kasar a yakin duniyar na 2 kafin yin jawabi.

A Faransa ma an takaita bikin da za a yi, amma hakan bai hana shugaba Emmanuel Macron gudanar da wani taro a fadar Champs-Elysees ba.

A Birtaniya Sarauniya Elizabeth za ta yi jawabi ga al’ummar kasar da misalign karfe 9 na dare, wanda zai yi daidai lokacin da mahaifinta Sarki George na 6 yayi jawabin samun nasarar yakin a shekarar 1945, yayinda dan ta Yarima Charles zai karanta wani sashi na rubutun da Sarkin yayi a kundin ajiye bayanansa a gaban ginin Fadar Buckingham.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.