Amurka-Turai

Bakuwar cuta mai alaka da coronavirus ta soma halaka yara a Turai

Hoton birnin New York dake Amurka daga nesa.
Hoton birnin New York dake Amurka daga nesa. CLARY AFP/File

Gwamnan birnin New York dake Amurka Andrew Cuomo, ya sanar da mutuwar wani karamin yaro mai shekaru 5, bayan fama da wata bakuwar cuta da ta haifar da kumburi a gefen zuciyarsa, cutar da masana suka ce tana da alaka da annobar coronavirus.

Talla

Gwamnan wanda yace tun a ranar Alhamis yaron ya mutu, ya kara da cewar yanzu haka akwai wasu karin yaran 73 da suka kamu da bakuwar cutar mai alaka da coronavirus.

A karshen watan Afrilu hukumomin lafiya a Birtaniya da Faransa suka soma shelar bayyanar bakuwar cutar dake addabar kananan yara da kwararru suka alakanta ta da cutar coronavirus.

Tun cikin watan na Afrilu hukumomin lafiyar na Birtaniya da Faransa suka sanar da cewa an kwantar da gwamman kananan yara a asibiti sakamakon fama da bakuwar cutar, wadda kawo yanzu ba a sanya mata suna ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.