Coronavirus-Amurka

Salon Trump wajen yakar corona annoba ce mai zaman kanta - Obama

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama tare da shugaba mai ci Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama tare da shugaba mai ci Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya caccaki Donald Trump kan yadda yake tunkarar annobar COVID-19 wadda tayi sanadiyar rasa rayukan dimbin Amurkawa, inda ya bayyana shi a matsayin babban bala’i.

Talla

A wata tattaunawa da Obama yayi da tsoffin jami’an gwamnatin sa da aka nada, tsohon shugaban ya bayyana takaici kan yadda ma’aikatar shari’a ta yafewa tsohon mai baiwa shugaba Trump shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn laifin da yayi, duk da amsa laifin san a yiwa hukumar FBI karya kan ganawa da jami’an gwamnatin Rasha.

Sakon na Obama ya bukaci tsoffin jami’an gwamnatin sa da su hada hannu da shi wajen goyawa Joe Biden baya a karawar da za suyi da shugaba Donald Trump a zaben watan Nuwamba.

Obama ya bayyanawa tsoffin jami’an nasa cewar bukatar su itace kawo sauyi wajen kawar da shugabancin da ake nuna san kai, kabilanci, raba kan jama’a da kuma kallon sauran jama’a a matsayin abokan gaba.

Tsohon shugaban yace hakan ya sa gwamnati ta gaza wajen tinkarar matsalar annobar COVID-19 wadda ta girma a duniya har ta yiwa Amurkawa illa wajen lakume rayukan mutane sama da 77,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.