Coronavirus

Coronavirus ta halaka karin Amurkawa dubu 1 da 635 a sa'o'i 24

Jami'an lafiya a asibitin Wyckoff dake Brooklyn a birnin New York na Amurka.
Jami'an lafiya a asibitin Wyckoff dake Brooklyn a birnin New York na Amurka. AFP Photo/Bryan R. Smith

Alkalumman hukumomin lafiya da jami’ar John Hopkins ta Amurka ke tattarawa sun nuna cewar, annobar coronavirus ta kashe karin mutane dubu 1 da 568 a kasar cikin awanni 24 da suka gabata.

Talla

Sabbin alkalumman ya sanya jumillar wadanda annobar ta halaka a Amurka kaiwa dubu 78 da 746, yayinda kuma ayawan wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai miliyan 1 da dubu 309 da 164.

Yanzu haka dai yawan mutanen da annobar COVID-19 ta halaka a fadin dunya ya haura dubu 277 daga cikin mutane miliyan 4 da dubu 1 da 437 da suka kamu, daga cikinsu kuma miliyan 1 da dubu 312 da 900 sun warke.

Annobar tafi muni a nahiyar Turai, inda ta halaka sama da mutane dubu 155 daga cikin sama da miliyan 1 da dubu 707 da suka kamu.

Amurka dai tafi kowace kasa fuskantar bala’in annobar coronavirus ko COVID-19, biye da ita kuma Birtaniya ce da ta rasa mutane dubu 31 da 587, sai Italiya mai mutane dubu 30 da 395, Spain ta rasa mutane dubu 26 da 478 yayinda a Faransa mutane dubu 26 da 310 suka mutu.

A nahiyar Afrika mutane dubu 2 da 160 annobar COVID-19 ta halaka, daga cikin dubu 59 da 254 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.