Yawan mutanen da annobar corona ke halakawa a Faransa ya ragu
Wallafawa ranar:
Hukumomin Lafiya a Faransa a dazunnan sun ce mutum 80 annobar coronavirus ta halaka cikin sa’o’i 24 da suka gabata, adadi mafi karanci na mamatan da kasar ta gani cikin wata guda, tun bayan barkewar annobar murar a cikinta.
Alkalumman sun kuma nuna cewar an samu raguwar adadin mutanen da annobar ke tilasta gaggawar garzayawa dasu zuwa sashin bada kulawa ta musamman dalilin shiga halin rai kwakwai, mutu kwakwai saboda cutar.
Rabon da a samu karancin adadin mutanen da annobar coronavirus ta kashe a Faransa tun a farkon watan Afrilu.
Alkalumman jami’an lafiya a kasar ta Faransa sun ce jumillar mutane dubu 95 da 829 suka kamu da cutar corona, daga cikin kuma dubu 56 da 38 sun warke.
Daga ranar litinin 11 ga watan Mayu, gwamnatin Faransa za ta sassauta dokar hana fitar da ta shafe sama da makwanni 5 tana aiki a daukacin kasar, da a baya ta kafa don dakile yaduwar annobar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu