Rasha-Coronavirus

Akalla 'Yan Rasha dubu 10 ke kamuwa da corona duk rana cikin mako 1

Motar feshin sinadaran kashe kwayoyin cutar coronavirus a Moscow, babban birnin kasar Russia. 1 ga watan Mayu, 2020.
Motar feshin sinadaran kashe kwayoyin cutar coronavirus a Moscow, babban birnin kasar Russia. 1 ga watan Mayu, 2020. Sergei Kiselyov/Moscow News Agency/REUTERS

Yawan masu cutar coronavirus a Rasha ya haura dubu 200, kamar yadda hukumomin lafiyar a kasar suka tabbatar a yau Lahadi.

Talla

Jumillar adadin masu cutar a Rasha ya kai dubu 209 da 688 ne, bayan samun karin ‘yan kasar dubu 11 da guda 12 da suka kamu da cutar ta coronavirus cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Kawo yanzu dai an shafe mako guda a Rasha gwaji na tabbatar da cewa ‘yan kasar sama da dubu 10 ke kamuwa da coronavirus a kullum.

Sai dai jami’an lafiya sun danganta hauhawar adadin wadanda annobar ke harba da yadda gwamnatin Rasha ta tashi tsaye wajen kara yawan mutanen da ake yiwa gwaji, inda kawo yanzu aka gwada akalla ‘yan kasar miliyan 5 da dubu 400.

Alkalumman jami’an lafiya a baya bayan nan sun nuna cewar mutane dubu 1 da 915 annobar coronavirus ta halaka Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.