Turai

Coronavirus: Kasashen Turai sun fara sassauta dokar hana fita

Wani yankin birnin Madrid bayan soma sassauta dokar hana a kasar Spain zirga-zirga.
Wani yankin birnin Madrid bayan soma sassauta dokar hana a kasar Spain zirga-zirga. REUTERS/Sergio Perez

Galibin kasashen nahiyar Turai sun fara sassauta dokar hana jama'a fita, wadda a baya suka kafa don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

Kasashen da suka sassaucin dokar hana fitar ya soma aiki a yau Litinin sun hada da Faransa da kuma Belgium.

A Faransa, shagunan gyaran gashi dana sayar da kayan sawa da littattafai da sauran muhimman kayayyakin bukata sun samu budewa bayan shafe makwanni sama da 5 a rufe.

Sai dai janye dokar hana zirga-zirgar bai shafi gidajen cin abinci, shagunan barasa da gidajen kallo ba, wadanda za su ci gaba da kasancewa a kulle.

A bangaren makarantu kuwa, gwamnatin Faransa ta baiwa kowace makaranta karbar kaso kadan daga dalibanta don kaucewa cinkoso a dakunan bayar da da darasu, yayinda aka sanyawa jama'a dokar tilasta amfani da kyalle ko takunkumin rufe baki da hanci a fadin kasar, zalika ba za su rika tafiyar da ta haura kilomita 100 daga gidajensu ba.

Sauran kasashen da suka sassauta dokar hana fitar a nahiyar Turai sun hada da Belgium sai dai matakin bai shafi makarantun kasar ba, yayinda su kuma Netherlands da Switzerland suka bada damar bude gidajen abinci amma da sharadin mutane fiye da 5 ba za su shiga a lokaci guda ba.

Sauran kasashen sun hada da Spain wadda ta ce sassaucin dokar bai shafi biranen Madrid da Barcelona ba, sai Birtaniya da Italiya, wadanda suma sassaucin bai shafi makarantu ba, sai kuma Jamus Austria, Poland, Norway, Croatia da Girka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI