Brazil

Coronavirus tafi yiwa Brazil barna fiye da kowace kasa a yankin Latin

Ma'aikatan wata makabarta a birnin Rio de Janeiro yayin adana gawar daya daga cikin mutanen da annobar coronavirus ta halaka a Brazil.  9/5/2020.
Ma'aikatan wata makabarta a birnin Rio de Janeiro yayin adana gawar daya daga cikin mutanen da annobar coronavirus ta halaka a Brazil. 9/5/2020. AFP

Ma'aikatar lafiyar Brazil tace adadin mutanen da annobar coronavirus ta halaka a kasar ya zarta dubu 10.

Talla

Alkalumman baya bayan nan daga kasar ta Brazil sun ce jumillar mutane dubu 155, 939 suka kamu da cutar coronavirus, daga cikinsu kuma dubu 10 da 627 sun rasa rayukansu.

Sai dai kwararru kan kimiyya sun yi gargadin adadin wadanda annobar za ta rutsa da su a kasar Brazil zai iya ninkawa sau 15 ko 20 nan da ‘yan makwanni, ganin yadda kasar ta gaza daukar matakan gaggauta yiwa mutane masu yawa gwajin cutar.

Akalla mutane dubu 3,600 suka rasa rayukansu a jihar Sao Paulo dake kudu masu gabashin kasar ta Brazil, yankin dake dauke da mutane kusan miliyan 46, inda kawo yanzu sama da mutane dubu 44,400 sun harbu da cutar.

Ita kuwa makociyar jihar Rio de Janeiro mai dauke da mutane sama da miliyan 16 ta samu adadin mamata dubu 1 da 653, wasu dubu 16 da 929 kuma sun harbu da cutar ta COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI