Faransa

Karfin annobar COVID-19 na raguwa a Faransa bayan halaka mutum 27,000

Wasu ma'aikatan jinya a asibitin Floreal dake garin Bagnolet a gaf da birnin Paris, yayin kula da mai cutar Covid-19. 8/4/2020.
Wasu ma'aikatan jinya a asibitin Floreal dake garin Bagnolet a gaf da birnin Paris, yayin kula da mai cutar Covid-19. 8/4/2020. © Ludovic Marin / AFP

Adadin mutanen da annobar coronavirus ke kashewa duk rana a Faransa na cigaba da raguwa, koda yake za a iya cewa cikin yanayi na hawa da sauka.

Talla

A larabar nan da ta gabata ma’aikatar lafiyar Faransa tace mutane 83 cutar ta halaka a sa’o’i 24, sabanin ranar talata da mutane 348 suka mutu dalilin annobar a kasar.

Yanzu haka jumillar yawan rayukan da cutar ta aika lahira a Faransar ya kai dubu 27 da 74, daga cikin dubu 140 da 734 da suka kamu.

Kididdigar hukummin lafiya a a baya bayan nan, ta nuna cewar kawo yanzu annobar coronavirus ta halaka jumillar mutane dubu 160 da 455 a nahiyar Turai, inda kashi 3 bisa 4 na mamatan suka fito daga kasashen Birtaniya, Italiya, Spain da kuma Faransa.

Alkalumman hukumomin lafiyar sun kuma ce adadin wadanda suka kamu da cutar a nahiyar Turan ya kai miliyan 1 da dubu 798 da 209.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.