Amurka

Bakuwar cuta mai alaka da coronavirus ta soma karfi a Turai da Amurka

Wata malamar makaranta a birnin Brussels yayin gwada zafin jikin daya daga cikin dalibanta saboda cutar coronavirus, bayan komawa makaranta.
Wata malamar makaranta a birnin Brussels yayin gwada zafin jikin daya daga cikin dalibanta saboda cutar coronavirus, bayan komawa makaranta. REUTERS/Johanna Geron

Hukumomin Lafiya na Amurka sun yi gargadi game da wata sabuwar cuta mai alaka da coronavirus da ke addabar kananan yara, wadda tuni ta soma sanadin mutuwarsu.

Talla

Hukumar Yaki da Cutuka ta Amurka, ta bayyana cutar a matsayin wadda ke haddasa kumburi a cikin jikin kananan yaran, wadda kuma a karshen watan Afrilun da ya gabata aka fara gano ta a Birtaniya, kafin daga bisani ma’aikatar lafiyar Faransa ta bayyana bullar bakuwar cutar a kasar.

Alamomin bakuwar cutar dai sun hada da zazzabi da kumburin wasu sassan cikin jikin dan adam, lamarin da ke haddasa tsananin rashin lafiyar da ke kai ga kwantar da mutum a asibiti.

A birnin New York na Amurka, an bada rahoton cewa, cutar ta kama yara akalla 100 tare da kashe uku daga cikinsu.

Likitocin da ke kula da masu dauke da wannan cuta, sun ce, wani lokacin masu fama da ita na nuna irin alamun cutar da ake kira ‘Kawasaki’ wadda ke haddasa kumburin magudanan jini a cikin jikin dan adam.

Sai dai kawo yanzu babu cikakkiyar masaniya kan ko wannan sabuwar cuta na shafar hatta manya masu yawan shekaru kamar yadda Hukumar Yaki da Cutuka ta Amurka ta ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.