Faransa-Rwanda

Faransa ta kama daya daga cikin mutanen da suka haddasa kisan kiyashin Rwanda

Wasu mutane a nahiyar Afrika yayin karanta labarin wata jaridar kasar Kenya a 2002, na bada sammacin kama Félicien Kabuga mutumin dake cikin jiga-jigan 'yan kasar Rwanda da suka hadda kisan kiyashin da aka yiwa 'yan kabilar Tutsi.
Wasu mutane a nahiyar Afrika yayin karanta labarin wata jaridar kasar Kenya a 2002, na bada sammacin kama Félicien Kabuga mutumin dake cikin jiga-jigan 'yan kasar Rwanda da suka hadda kisan kiyashin da aka yiwa 'yan kabilar Tutsi. REUTERS / George Mulal

‘Yan sandan Faransa sun kama daya daga cikin jiga-jigan mutanen da ake tuhuma da hannu wajen assasa kisan kare dangin da aka yi a Rwanda cikin shekarar 1994.

Talla

Jami’an tsaron na Faransa sun bayyana mutumin mai suna Felicien Kabuga a matsayin daya daga cikin manyan attajiran Rwanda a waccan lokacin, wanda kuma shi ne ya bada kudaden da aka kafa kungiyar 'Intrahamwe' da ta kunshi ‘yan kabilar Hutu, wadda ta halaka ‘yan kabilar Tutsi kimanin dubu 800, gami da kashe wasu mutanen daga kabilar Hutun masu sassaucin ra'ayi akalla 100.

Hukumomin tsaro sun ce an kame Felicien Kabuga ne a arewacin birnin Paris, bayan shafe shekaru 25 yana gujewa shari’a.

Kafin kama shi a Faransa, bayanai sun ce a tsawon shekarun da yayi yana wasan buya da jami’an tsaro, Kabuga ya zauna a Jamus, Belgium, Switzerland, Kenya da kuma Jamhuriyar Congo.

Tun a shekarar 1997 kotun sauraron kararraki kan kisan kare dangin Rwanda da majalisar dinkin duniya ta kafa, ta tuhumi Felicien Kabuga da laifuka 7 ciki harda zama kashin bayan kisan kiyashin da aka yiwa ‘yan kabilar Tutsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.