Brazil-Coronavirus

Takaddama kan sahihancin coronavirus ya sanya ministan lafiyar Brazil yin murabus

Ministan lafiyar Brazil da ya ajiye aikinsa Nelson Teich daga bangaren hagu, tare da shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro.  17/4/2020
Ministan lafiyar Brazil da ya ajiye aikinsa Nelson Teich daga bangaren hagu, tare da shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro. 17/4/2020 EVARISTO SA AFP/File

Ministan lafiyar Brazil Nelson Teich ya sauka daga mukaminsa kasa da wata guda bayan nada shi akai, saboda abinda ya kira sabani tsakaninsa da shugaba Jair Bolsonaro wajen tunkarar annobar coronavirus dake cigaba da hallaka jama’a a cikin kasar.

Talla

Wannan ya kawo adadin ministocin lafiyar Brazil guda 2 wadanda suka ajiye ayyukansu, saboda sabanin da suke da shugaban kasar, wanda bai yadda da sahihancin annobar ta coronavirus ba.

Ya zuwa yanzu Brazil ce kasa ta 6 a duniya da tafi samun wadanda suka mutu sakamakon annobar, wadanda suka zarce 16,000, daga cikin akalla mutane dubu 219 da suka kamu.

Yawan wadanda suka warke daga cutar ta coronavirus a kasar ta Brazil kuma a yanzu ya kai dubu 84, 970.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.