Amurka

Trump ya kori Sifeto Janar dake tuhumar Pompeo da saba ka'idar aiki

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori wani babban jami’i dake rike da mukamin Sifeto Janar, wato Steve Linick saboda kaddamar da binciken da yayi kan sakataren harkokin waje Mike Pompeo dangane da saba ka’idar aiki.

Talla

Rahotanni sun ce Linick na gudanar da bincike ne kan yadda Pompeo ke tafiye tafiye da matarsa da kuma karensu zuwa kasashen duniya, matakin da ya sabawa aikin gwamnatin Amurka.

Wasu daga cikin jami’an tsaron Amurka dake kare lafiyar sakataren suka gabatar da korafi cewar, yana sa su aikin da ba nasu ba wajen kare matarsa da kuma karensu da yake yawo da shi kasashen duniya, abinda yasa Linick ya fara bincike kan lamarin.

Pompeo na daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka da suka fi kusa da shugaba Donald Trump, kuma wasu na kallonsa a matsayin wanda yake share hanyar tsayawa takarar zabe nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.