Faransa-Jamus

Faransa da Jamus sun gabatar da shirin tallafin euro biliyan 500 ga Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic MARIN / POOL / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun gabatarwa kungiyar Turai wani shirin tallafin kudade da yawansu zai kai Euro bilyan 500 domin farfado da tattalin arzikin nahiyar Turai, wanda ya yi matukar girgiza sakamakon annobar COVID-19.

Talla

Shugaban Faransa Macron, yace akwai bukatar gaggauta amincewa da shirin tallafin kudaden dake a matsayin rance domin cike gibin da tattalin arzikin kasashen Turai ke fuskanta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron kan shirinsa da Jamus na samar tallafin euro biliyan 50 ga tattalin arzikin Turai

Shugaba Macron ya kara da cewar, ya zama dole hada kai da kuma sake karfafa fannin lafiyar Turai ya zama babban abinda nahiyar tasa a gaba daga yanzu.

Macron yayi gargadin ne, yayinda yake amsa cewar gwamnatocin kasashen Turai dama kungiyar kasashen nahiyar sun gaza wajen daukar matakan dakile yaduwar annobar coronavirus da ta halaka sama da mutane dubu 167 a Turan kadai, daga cikin kusan mutane dubu 316 da ta kashe a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.