Faransa-Coronavirus

Faransa ta samar da manhajar gano masu dauke da cutar coronavirus

Wata mata yayin nazarin shafin sabuwar manhajar bada bayanai kan cutar coronavirus.
Wata mata yayin nazarin shafin sabuwar manhajar bada bayanai kan cutar coronavirus. Catherine LAI/AFP File

Kasar Faransa ta yi gaban kanta wajen kera manhajar gano masu dauke da cutar coronavirus duk da fargabar da manyan kamfanonin fasahar sadarwa na Google da Apple suka nuna, dangane da yiwa masu amfani da manhajar kutse.

Talla

Ana ci gaba da tafka muhawara a Faransa da wasu kasashen Turai kan yadda ya kamata a samar da manhajar da ke iya zakulo masu dauke da cutar coronavirus, inda wasu ke ganin cewa, akwai bukatar yin taka-tsan-tsan don gujewa afkawa cikin bayanan asirin jama’a.

Kamfanonin Apple da Google dai sun hakikance cewa, ya kamata a bi tsarin da a za a kauce yiwa masu wayoyin hannu kutse, a yunkurin gano mutanen da suka kamu da cutar, amma Faransa na fatan samun cikakkiyar damar bibiyar wadanda suka kamu kai tsaye daga wata katafariyar na’urarta karkashin kulawar ma’aikatar lafiyar kasar.

Manhajar dai ta kashi gida biyu, ta farko na baiwa masu wayoyin hannu ‘yancin sanar da hukumomi kan ko sun harbu da cutar da kuma adadin mutanen da suka yi mu’amala dasu, yayinda a mahnaja ta biyu, hukumomi kadai ke da damar bibiyar halin da jama’a ke ciki, tare da ba su umarnin killace kansu da zarar sun harbu, kuma wannan tsarin ne Faransa ta zaba.

Tuni kasashe da dama suka fara amfanin da irin wannan manhajar, wadda aka kera don dakile yaduwar coronavirus a duniya.

A watan jiya ne Google da Apple suka hada guiwa domin su ma su samar da irin wannan manhajar wadda suka ce za su saki nan gaba a cikin wannan wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.