Brazil-Coronavirus

'Yan Brazil kusan dubu 20 sun kamu da cutar corona a rana 1

Rio de Janeiro: Wasu jami'an lafiya dauke da gawar daya daga cikin dubban mutanen da annobar coronavirus ta kashe a Brazil. 18/5/2020
Rio de Janeiro: Wasu jami'an lafiya dauke da gawar daya daga cikin dubban mutanen da annobar coronavirus ta kashe a Brazil. 18/5/2020 REUTERS/Ricardo Moraes

Brazil ta shiga jerin kasashen da annobar coronavirus ta fi yin ta’adi a cikinsu, inda a yanzu haka ta zama kasa ta uku a duniya ta tafi yawan masu wadanda suka kamu da cutar, idan aka dauke Amurka da Rasha.

Talla

Alkalumman da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar a baya bayan nan sun nuna cewar, mutane dubu 19 da 951 suka kamu da coronavirus, yayinda kuma annobar ta halaka wasu 888 a ranar 1.

A jumlace yawan mutanen da cutar ta halaka a Brazil ya kai dubu 18 da 859, adadin masu dauke da cutar kuma ya karu zuwa dubu 291 da 579.

Yanzu haka dai Brazil ke kan gaba wajen fuskantar kaifin annobar coronavirus a nahiyar Kudancin Amurka, yayinda kasar Peru ke biye da ita, bayan rasa mutane dubu 3,024 daga cikin mutane dubu 104 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI