Spain

Mun yi kuskure wajen kidayar mutanen da annobar coronavirus ta halaka - Spain

Wasu ma'aiakatan lafiya a birnin Madrid, tare da mai jinyar cutar coronavirus zaune bisa keken guragu
Wasu ma'aiakatan lafiya a birnin Madrid, tare da mai jinyar cutar coronavirus zaune bisa keken guragu AFP

Gwamnatin Spain ta rage adadin jumillar wadanda a baya tace annobar coronavirus ta halaka a kasar da kusan mutane dubu 2.

Talla

A baya dai jumillar mutane dubu 28 da 772 ma’iakatar lafiyar kasar tace sun mutu a dalilin annobar, sai dai a yanzu adadin ya koma dubu 26, 834.

Shugaban gudanarwar ma’aikatar lafiyar Spain Fernando Simon yace an samu sauyin ne, sakamakon sake bin kidayar mamatan da aka yi, inda aka gano an kidaya wasu mutanen sau 2 ko sama da haka.

Zalika an sake nazari wajen tantance mutanen da aka yi kuskuren bayyana cewar annobar coronavirus ce ta halaka su, bayanda karin bincike ya nuna cewar wasu cutukan na daban suka kashe su.

Yanzu haka dai sabon rahoton hukumomin kasa da kasa suka fitar a jiya kan annobar coronavirus ya ce a halin yanzu cutar ta halaka jumillar mutane dubu 344 da 107 a fadin duniya, daga cikin kusan mutane miliyan 5 da rabi suka kamu da cutar.

Har yanzu dai a matakin kasa coronavirus ta fi yin ta’adi a Amurka inda ta kashe mutane dubu 97 da 948, daga cikin miliyan 1 da dubu 653 da 390 da suka kamu, yayinda a matakin nahiyar cutar tafi yiwa Turai barna, inda ta halaka mutane dubu 172 da 575, kasashen Birtaniya, Italiya, faransa da kuma Spain ke kan gaba wajen fuskantar munin annobar a nahiyar.

A nahiyar Kudancin Amurka da yankin Caribbean mutane dubu 40 da 318 cutar ta kashe, yayinda Afrika ta rasa mutane dubu 3 da 398.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI