Faransa

Faransa ta haramta amfani da hydroxychloroquine kan masu cutar coronavirus

Ministan lafiyar Faransa Olivier Veran.
Ministan lafiyar Faransa Olivier Veran. REUTERS/Charles Platiau/File Photo

Gwamnatin Faransa ta sanar da soke dokar da ta baiwa likitoci da sauran jami’an lafiya damar amfani da maganin hydroxychloroquine don warkar da masu fama da cutar COVID-19, bayan gano illar da nau’in maganin kan yi ga lafiyar bil’adama.

Talla

Nau’in maganin na hydroxychloroquine wanda shugaban Amurka ke ci gaba da kokarin ganin jami’an lafiya sun yi amfani da shi don magance coronavirus da ke ci gaba da kisa a duniya, masana sun bayyana cewa shi kansa nau’in maganin ya haddasa asarar rayukan mutane da dama, wadanda suka yi amfani da shi wajen rigakafin cutar ta corona.

Sashin binciken ma’aikatar lafiyar Faransa dake sanar da matakin a jiya Laraba, ya ce tun bayan binciken da dakunan gwajin nahiyar Turai suka gudanar a Lahadin da ta gabata, a hukumance aka dakatar da amfani da nau’in maganin, yayinda ya zama doka a Faransa daga ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Matakin na Faransa wanda ya fara aiki nan take, shi ne yunkuri na farko da wata kasa ta yi tun bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da illar maganin tare da dakatar da gwajin da ta ke yi dashi kan masu cutar.

Soke dokar ta Faransa bayan yiwa marasa lafiya fiye da dubu hudu amfani da nau’in maganin na nuni da cewa daga yanzu amfani da nau’in maganin na Hydroxychloroquine ta kowacce fuska ya zama haramtaccen lamari a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.