Faransa-Coronavirus

Faransa ta sake bude gidajen abinci da na barasa bayan shafe makwanni a garkame

Fira Ministan Faransa, Edouard Philippe.
Fira Ministan Faransa, Edouard Philippe. Christophe Ena / Pool via REUTERS

Gwamnatin Faransa ta sanar da bude manyan gidajen abinci, wuraren shan barasa, da kuma gidajen dana kayan tarihi, bayan shafe makwanni da dama a rufe saboda annobar coronavirus.

Talla

Yayin sanar da matakin janye dokar kulle wuraren hada-hadar, Fira Minista Edouard Philippe yace matakin zai soma aiki ne daga ranar 2 ga watan Yuni mai kamawa.

Fira Ministan ya kuma bayyana soke dokar takaita baluguron da aka baiwa jama’a damar yi na tsawon kilomita 100 kawai, inda a yanzu tafiye-tafiye cikin kasar ta Faransa za su koma kamar yadda aka saba.

Zuwa yanzu mutane dubu 28 da 662, annobar coronavirus ta halaka a Faransa, daga cikin mutane dubu 186 da 238 da suka kamu, yayinda akalla dubu 67 suka warke.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.