Faransa

Kamfanin kera motocin Renault zai sallami ma'aikata dubu 15

Wani sashe na kamfanin kera motin Renault dake Faransa.
Wani sashe na kamfanin kera motin Renault dake Faransa. Martin BUREAU / AFP

Kamfanin kera motocin Renault dake Faransa zai sallami ma’aikatansa kimanin dubu 15 a fadin duniya, ciki harda dubu 4 da 600 dake kasar.

Talla

Majiyoyin da suka tabbatar da shirin sallamar dubban ma'aikatan ga kamfanin dillancin labarai na AFP, sun ce a yau Juma’a ake sa ran kamfanin na Renault zai sanar da shirin nasa a hukumance.

Matakin kamfanin motocin Renault dai bangare ne na shirin tsuke bakin aljihunsa, ta hanyar rage adadin kudaden gudanarwar ayyukansa da yake kashewa da adadin euro biliyan 2 cikin akalla shekaru 3.

Sallamar dubban ma’aikatan na zuwa ne bayanda takwarorin kamfanin na Renault a fannin kera motoci da wasu na sufurin ababen hawa na motoci da jiragen sama, ke sallamar dubban ma’aikatansu, saboda tasirin annobar coronavirus da ta durkusar da tattalin arzikinsu, bayan tilastawa gwamnatoci killace fiye da rabin al’ummar duniya a watannin da suka gabata.

A ranar Talata 26 ga watan Mayu, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana shirin gwamnatinsa na ware euro biliyan 8 domin farfado da kamfanonin kera motocin kasar da suka durkushe saboda tasirin annobar coronavirus da ta tagayyara tattalin arzikin duniya, bayan tilasta killace biliyoyin mutane da kuma rufe kamfanonin da ta yi.

Shugaba Macron yace tallafin ya kunshi euro biliyan guda da aka ware domin karfafa sayen motoci masu amfani da lantarki maimakon man fetur, domin cimma burin Faransa na kera ire-iren motocin akalla miliyan 1 nan da shekarar 2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.