Amurka

Dubban Amurkawa na zanga-zanga kan mutuwar wani bakar fata a hannun 'yan sanda

Yadda masu zanga-zanga kan mutuwar George Floyd a hannun 'yan sanda suka cinnawa wurare da dama wuta a birnin Minneapolis. 28/52020.
Yadda masu zanga-zanga kan mutuwar George Floyd a hannun 'yan sanda suka cinnawa wurare da dama wuta a birnin Minneapolis. 28/52020. REUTERS/Nicholas Pfosi

Dubban Amurkawa na cigaba da yin zanga-zanga a biranen kasar da suka hada da New York, Washington, Atlanta, Los Angeles da Minneapolis dake jihar Minnesota, inda boren ya samo asali, bisa kashe wani bakar fata da ake zargin wani dan sanda farar fata da yi.

Talla

A jiya Juma’a tsaron Amurka suka kame dan sanda Derek Chauvin, bisa tuhumarsa da zama sanadin mutuwar George Lloyd wani ba-Amurke bakar fata a garin Minneapolis dake jihar ta Minnesota.

Tun a ranar litinin ne dai wani bidiyon yadda dan sandan ya taka wuyan bakar fatar da gwiwarsa tsawon mintuna, wanda daga bisani ya mutu ke yawo, abinda ya janyo gudanar da jerin zanga-zangar tilastawa hukumomin tsaro hukunta jami’in dan sandan.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Amurka a ranar Talata, ta kori dukkanin jami’anta guda hudu da suka bayyana a faifan bidiyon dake nuna yadda abokin aikinsu Derek Chauvin ya ci zarafin George Lloyd ta hanyar taka masa wuya.

Sai dai duk da kamen da kuma tuhumar dan sandan da hukumomin tsaron Amurka suka yi, boren da masu zanga-zangar ke yi na cigaba da gudana, inda a Atlanta masu boren suka kone wasu motocin ‘yan sanda, yayinda Minneapolis cibiyar zanga-zangar gwamnati ta kafa dokar hana zirga-zirga, amma duk da hakan sai da aka samu arrangama tsakanin ‘yan sanda da masu bore kwana na 3 a jere.

Yanzu haka dai an girke dakarun sojin Amurka a titunan birnin na Minneapolis domin tabbatar da doka da oda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.