Faransa za ta haramta salon shakar da 'yan sanda ke yiwa masu laifi

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Christophe Castaner.
Ministan harkokin cikin gidan Faransa Christophe Castaner. FranceTV

Gwamnatin Faransa ta sha alwashin dakatar da dokar da ta baiwa ‘yansanda damar amfani da wani salon shake wuya yayin tuhuma ko kuma kamen wanda ake zargi da aikata laifi, matakin da ke zuwa bayan zanga-zangar Amurka kan kisan bakar fata George Floyd da ta tunawa Faransa kisan Adama Traore.

Talla

Acewar rundunar ‘yansanda Faransa bara kadai ta samu korafe-korafe dubu 1 da 500 masu alaka da zargin cin zarafi da ‘yansanda ke yiwa fararen hula a kasar.

Zanga-zangar ta Amurka kan kisan Floyd dai tuni ta haddasa yamutsu a sassan duniya, kuma kasashen da lamarin ya fi tsananta har da Faransa, kasar da zanga-zangar ta tunawa al’umma da kisan da ‘yansanda suka yiwa matashi Adama Traore mai shekaru 24 shekarar 2016, batun da ya kara futo da irin cin mutunci da kuma nuna wariyar da ‘yansandan kasar ke nunawa bakar fata.

Ministan harkokin cikin gida na Faransar Christophe Castaner wanda ke kokarin kwantar da hankalin masu zanga-zangar don gudun sake faruwar kakkarfar zangar-zangar makamanciyar ta 2016, ya ce dole ne su dakatar da dokar ta yiwa mutane salon shakar wadda a makamanciyarta ne Floyd ya rasa ransa a hannun ‘yansandan na Minnesota.

A jawabin ministan cikin gidan na Faransa, ya ce babu hurumin nuna wariya cikin rundunar ‘yansada yayinda ya yi umarnin hana koyar da salon shakar a makarantun horar da ‘yansanda da Jami’an tsaro na Jandarma da ke fadin kasar.

Christophe Castaner ya ce ba kadai yin tir da salon shakar ne zai magance rasa rayukan mutane ba, abu mafi kyawu shi ne dakatar da dokar da ta baiwa ‘yansanda yin salon shakar dungurugum.

Salon shakar wadda ake kira Chokehold a turance, jami’an tsaron kanyi amfani da hannunsu na dama ne wajen shako wuyan wanda ake zargi da aikata laifi ko kuma ake tuhumarsa a ofishinsu, shakar da masana kiwon lafiya suka bayyana cewa takan hana gudanyar jini da iska ta yadda ta ke iya kashe mutum a kankanin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.