Mutane dubu 800 za su rasa ayyukansu a Faransa
Gwamnatin Faransa ta ce, akwai yiwuwar mutane dubu 800 za su rasa guraben ayyukansu nan da watanni kalilan masu zuwa, a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke farfadowa bayan ya durkushe saboda annobar coronavirus.
Wallafawa ranar:
Ministan Kudin Faransa, Bruno Le Maire ya yi wannan gargadi a yayin jawabi ga Kwamitin Kudi na Majalisar Dokokin kasar, yana mai cewa, hasashensu ya nuna cewa, mutane dubu 800 za su rasa ayyukansu , wato kwatankwacin kashi 2.8 na daukacin ma’aikatan da ake da su a kasar.
Ministan ya ce, wannan al’amari abin dubawa ne, yayin da ya yi kira da a samar da wani gagarumin shirin tallafa wa al’umma musamman wadanda matsalar za ta shafa.
Tsare-tsaren da Ministan ke fatan a samar, sun hada da sassauta karbar kudin haraji ga kamfanoni da kuma bada ladar kudi ga kananan ma’aikata ‘yan koyo.
A ranar Talatar da ta gabata ne, Babban Bankin Faransa ya ce, akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar ya fadi kasa da kimakin kashi 10 biyo bayan dokar kulle jama’a a gidajensu da aka kafa don hana bazuwar annobar coronavirus a cikin watan Maris.
A cewar bankin na Faransa, tattalin arzikin kasar ba zai koma kamar yadda aka san shi ba kafin zuwan coronavirus har sai nan da tsakiyar shekarar 2022.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu