Faransa

Macron ya musanta rade-radin kiran zaben gaggawa a Faransa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Romain Ferré/RFI

Fadar Shugaban Faransa ta yi watsi da rade-radin cewar shugaba Emmanuel Macron na shirin kiran zaben gaggawa kamar yadda ake zargin cewar ya shaidawa manyan masu baiwa jam’iyyar sa gudumawa.

Talla

Jaridar Le Figaro ta ruwaito cewar shugaba Emmanuel Macron ya bayyana bukatar kiran zaben lokacin da ya ke gudanar da taro tare da wasu masu bada agaji na Jam’iyyar sa ta bidiyo lokacin da suka taru a London makwanni biyu da suka gabata.

Jaridar ta ce Macron ya shaidawa taron cewar zaben zai dada karfafa sahihancin kujerar sa a daidai lokacin da kasar ke shirin bude kofofin ta daga annobar COVID-19 wadda ta yiwa kasar illa.

Jam’iyyar Macron ta rasa rinjayen da ta ke da shi a Majalisa a watan jiya lokacin da 'yan Majalisu da dama suka balle domin kafa kawance mai zaman kan sa abinda ke nuna raguwar farin jinin sa.

Sai dai fadar shugaban ta yi watsi da rahotan, inda ta ce babu inda shugaba Emmanuel Macron ya ce zai sauka daga kujerarsa, kuma bai gudanar da wani taro ba kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Rahotanni sun ce ana saran shugaba Macron ya yiwa al’ummar kasar jawabi ranar lahadi mai zuwa, irin san a 4 tun bayan barkewar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI