Macron ya yi tir ga masu nuna wariyar launin fata

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Romain Ferré/RFI

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da masu nuna banbancin launin fata abinda ya kira a matsayin zagon kasa ga gwagwarmayar kafa ‘yancin kasa.

Talla

Yayin da yake tsokaci kan zanga zangar adawa da kisan gillar da aka yiwa George Floyd a Amurka wanda ya gamu da suka daga sassan duniya da kuma rawar da Yan Sanda ke takawa, shugaba Emmanuel Macron ya bayyana nuna wariyar jinsi a matsayin wata sankarar dake yaki da ‘yancin Bil Adama.

A sanarwar da mai Magana da yawun sa Sibeth Ndiaye ta rabawa manema labarai, Macron ya bayyana wariyar jinsi a matsayin cutar da ta kama al’umma, inda ya bukaci jami’an sa da su tashi tsaye wajen yaki da ita.

Shugaban yayi watsi da masu zargin Yan Sandan Faransa da nuna halaye irin na wadanda suka kasha George Floyd a Amurka, inda yace Yan sandan Faransa na da kwarewar da ta dace wajen gudanar da ayyukan su.

Macron ya bukaci sake dabarun kamawa da kuma tsare wadanda ake zargi da aikata laifuffuka, yayin da ministan cikin gida Christophe Casterner ya sanar da dakatar da dabarar makure wuyar wanda ake zargi da aikata laifi da wasu jami’an Yan sanda ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI