Faransa
Kotun Faransa ta umarci bude kayan tarihin Mitterand don binciken kisan Rwanda
Babbar Kotun mulkin Faransa ta bada umurnin bude kayayyakin tarihin tsohon shugaban kasa Francois Mitterand domin baiwa wani mai bincike damar duba takardun da ke da nasaba da kisan kiyashin da akayi a kasar Rwanda a shekarar 1994.
Wallafawa ranar:
Talla
Kotun ta ce umurnin zai baiwa mai binciken Francois Graner damar nazarin bayanan asiri da za suyi karin haske kan kisan wanda jama’a ke so suji.
Zarge zarge da dama sun biyo bayan kisan kare dangin na Rwanda da kuma rawar da gwamnatin Faransa ta taka lokacin, abinda ya haifar da takaddama tsakanin kasashen biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu