Tarayyar Turai

kasashen turai 27 zasu samar da maganin corona na hadin gyuiwa.

hanyoyin samar da maganin riga-kafi na da tsawo, wani lokaci da wahala.
hanyoyin samar da maganin riga-kafi na da tsawo, wani lokaci da wahala. iStock / Neznam

Kasashen kungiyar tarayyar turai sun yanke shawarar hada karfi da karfe kan shirin samar da da wata cibiyar binciken magungunna da za ta samar da maganin cutar Covid-19. A yayin da kungiyar ta tarrayya turai za ta samar da kudaden tafiyar da aikin binciken.

Talla

Manufar hakan dai shine baiwa kungiyar damar samun karfin tunkarar annobar ne, da ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a nahiyar.

Kasashen 27 dai, duk sun goyi bayan shirin samar da maganin cutar ta COVID 19 da zai lakume kimanin euro biliyan 2.4 wajen kudanar da shi.

Nahiyar turai dai ita ce nahiyar da ta fi dandanar kudarta daga annobar ta Covid 19 da ta yiwa kasashen Faransa, Birtaniya, Italy, da kuma Spain mummunar illa, ta fannin hasarar rayuka da kuma tattalin arziki tun bayan bulluwarta a nahiya kimanin watanni 4 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI