Zanga zangar nuna adawa da muzgunawar 'yan sanda a Faransa.
Wallafawa ranar:
A yau ne a birnin Paris na kasar Faransa ake gudanar da jerin gwano nuna adawa da cin zarafin da ‘yan sanda ke yi a kasar, wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar ‘yan sanda kasar ke nuna bacin ranta kan kalaman ministan cikin gidan kasar dake jan hankalin ‘yan sandan da su guji nuna kabilanci a kasar.
‘Yan sandan dai, sun nuna bacin ransu kan furucin ministan cikin gidan Faransa Christophe Castaner, dake gargadin daukar matakan ladabtarwa kan duk wani dan sanda, da aka samu da laifin nuna kabilanci a kasar.
Furucin da ko kadan bai yi wa kungiyar maákatan yan sandan dadi ba.
Wanda ya sa a wannan mako, kungiyar ‘yan sanadan ansa ta yi kiran gudanar da jerin gwano, a jiya juma’a ‘yan sanda sun ka taru kan titin Champs-Elysées dake tsakkiyar birnin Paris, tare da jefar da sarkokin Ankwa a kasa.
wanan dai na zuwa ne domin nunawa maáikatar cikin gidan, rashin jin dadinsu kan abinda suka kira zarginsu da nuna kabilanci da ministan ya yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu