Kasashen Turai sun fara bude iyakokinsu

China ta fara gudanar da gagarumin gwajin cutar Korona bayan sake bullar cutar a Beijing
China ta fara gudanar da gagarumin gwajin cutar Korona bayan sake bullar cutar a Beijing AFP

Wasu kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU sun sake bude kan iyakokinsu ga takwarorinsu na Turai a wannan Litinin, bayan shafe watanni a rufe sanadiyar barkewar cutar Coronavirus, yayinda kasar China inda cutar ta samo asali ta fara killace wasu yankunanta kan fargaba sake barkewar COVID-19 a karo na biyu.

Talla

A sassa da dama na kasashen yankin Turai da annobar korona tayiwa mummnunar illa tun bayan bullarta, an fara samun saukin cutar a makwannin baya-bayan nan, inda gwamnatoci suka himmatu wajen sauƙaƙe dokokin kulle da suka sanya don hana bazuwar cutar ya haifar da mummunar koma bayan tattalin arziƙi.

Kasashen Beljiyam da Faransa da Jamus da Girka da kuma Ukraine na daga cikin wadanda suka sanar da bude kan iyakokinsu daga Litinin din nan, yayin da kasar Ingila ta bude shaguna da wuraren shakatawa karon farko tun daga watan Maris, kana Faransa ta saki mara ga gidajen shakatawa da na cin abinci a birnin Paris suka bude kofofinsu.

To sai dai, da alama tsugune bai kare ba a wasu sassan duniya, inda cutar ke tasri har yanzu, a Latin Amurka da kasashen Iran da Indiya da ake samun karuwar mace-mace da sabbin masu kamuwa da cutar na kara fito da kalubalen da duniya ke fuskanta na kokarin kawar da annobar cikin gajeren lokaci.

Kasar China inda cutar ta bulla a watan Disambar bara, ta sanar da killace wasu Karin unguwanni guda 10 a birnin Beijing tare da rufe kasuwanni da makarantu a Yankin Haidian, yayin da ta gano yaduwar cutar a kasuwar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI