Faransa

Jami'an gwamnatin Faransa 6 za su yi zaman yari kan badakalar cinikin makamai

Wata Kotu a Faransa ta bada umurnin daure wasu tsoffin manyan jami’an gwamnatin kasar 6 saboda samun su da laifin karbar cin hanci na miliyoyin euro sakamakon cinikin makamai tsakanin kasar da Pakistan da kuma Saudi Arabia a shekarar 1994.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/François Mori
Talla

Kotun ta zartas da hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 5 ga makusantan na tsohon Firaministan Faransar Edouard Balladur, tsohon shugaban da shima a bangare guda ke fuskantar tasa shari'ar kan yadda ya samar da kudin yakin neman zabensa, yayin zaben shugaban kasa na 1995 da ya sha kaye.

Wannnan dai shi ne karon farko da aka yanke hukunci kan wannan batu bayan shafe tsawon shekaru ana bincike tare da mabanbantan zaman kotu kan badakalar wadda aka yiwa lakabi da badakalar “Karashi” wadda ta shafi wasu manyan jami’an Faransa a gwamnatoci daban-daban tun daga kan marigayi shugaba Jacque Chirac har zuwa Nicola Sarkozy.

An dai fara bincike kan badakalar ne bayan harin Bom din birnin Karachi na Pakistan a shekarar 2002 da ya kashe mutane 15 ciki har da injiniyoyin Faransa 11, harin da ake kallo a matsayin martani ga matakin shugaba Jacque Chirac na dakatar da cinikin makaman bayan lashe zabe a wancan lokaci.

Cikin manyan jami’an da Kotun ta zartaswa hukunci har da da Nicolas Bazire, Manajan yakin neman zaben Balladur da Renaud Donnedieu de Vabres, tsohon mai ba da shawara ga ministan tsaro Francois Leotard sai kuma Thierry Gaubert, tsohon mataimaki ga ministan kasafin kudi na lokacin Nicolas Sarkozy da ya zama shugaban kasa a 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI