Faransa ta bayyana shakku kan kulluwar yarjejeniyar Birtaniya da EU
Wallafawa ranar:
Faransa ta ce bata da tabbacin cewar za’a iya kulla yarjejeniya tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya domin cigaba da hulda tare duk da ya ke bata bukatar ganin haka.
Ministan harkokin wajen Faransar Jean Yves Le Drian wanda ke bayyana hakan, ya ce ba za su iya kawar da shirin kasa kulla yarjejeniya ba duk da ya ke ba bukatar su bane, ganin yadda Birtanyar ke wasa da hankalin su.
Jawabin na Le Drian na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Emmanuel Macron ke shirin ziyarar birnin London a gobe Alhamis inda zai gana da Firaminista Boris Johnson.
Tun bayan ficewar Birtaniyar daga EU, har yanzu bangarorin biyu sun gaza jimma jituwa kan yarjejeniyar kasuwancin tsakaninsu, duk da cewa dai Birtaniyar na da zuwa nan da karshen shekarar nan kafin karewar wa'adinta na cin moriyar alakarta da kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu