Birtaniya-Coronavirus

Dexamethasone ya warkar da masu coronavirus dubu 2 a Birtaniya

Nau'in maganin dexamethasone da ya warkar da masu coronavirus dubu 2 a Birtaniya.
Nau'in maganin dexamethasone da ya warkar da masu coronavirus dubu 2 a Birtaniya. Reuters

Birtaniya ta sanar da shirin fara amfani da nau'in maganin Steroid dexamethasonedon warkar da masu coronavirus bayan wani binciken baya-bayan nan da ke nuna karfin maganin wajen iya warkar da cutar dai dai lokacin da duniya ke tsaka da fargabar sake juyowar cutar a karo na biyu.

Talla

Matakin Birtaniya kan rungumar amfani da nau'in maganin na Steriod dexamethasone na zuwa bayan binciken tawagar kwararru wajen samar da maganin karkashin jagorancin Jami'ar Oxford wanda ya gudanar da gwaji kan wasu masu fama da cutar ta coronavirus dubu 2 kuma aka samu nasarar warkewarsu.

Gwajin ya nuna cewa hatta marasa lafiyan da ke kwance a halin rai-kwa-kwai mutu kwa-kwai dama wadanda ke numfashi da taimakon na’ura, nau'in maganin na Dexamethasone ka iya warkar da su da akalla kashi 35.

Matt Hancock, Sakataren harkokin kiwon lafiya na Biritaniya ya ce, ba tare da wani bata lokaci ba, masu dauke annobar COVID-19 a fadin kasar za su fara karbar nau'in maganin.

Tuni masana, irinsu Farfesa Peter Horby, kwararre kan cututtuka masu yaduwa kuma malami a sashen nazarin magunguna na Jami'ar Oxford suka yaba wannan ci gaba da aka samu, inda ya ke cewa maganin zai amfani Duniya, dai-dai lokacin da kasashe suka fara fargabar sake barkewar cutar a karo na biyu, bayan da cutar ta sake bulla a kasar China inda ta faro cikin watan Disamban bara.

Zuwa yanzu dai fiye da mutun dubu dari 4 Coronavirus ta hallaka a sassan Duniya kaso mai yawa a nahiyar Turai da Amurka, inda ake da jumullar mutum miliyan 8 da dubu dari 3 da ke dauke da cutar ko da dai wasu mutum miliyan 3 sun warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI