Spain

Spain za ta karrama mamatan coronavirus

Jami'an Kiwon Lafiya na cikin wadanda suka sadaukar da rayukansu a yaki da coronavirus a Spain
Jami'an Kiwon Lafiya na cikin wadanda suka sadaukar da rayukansu a yaki da coronavirus a Spain AP

Kasar Spain ta ce, za ta karrama mutanen da annobar coronavirus ta kashe a kasar a ranar 16 ga watan gobe a bikin da ake sa ran shugabannin Kungiyar Kasashen Turai da na Hukumar Lafiya ta Duniya za su halarta.

Talla

Firaminista Pedro Sanchez ya ce,  za a gudanar da bikin na kasa domin girmama mamata 27,000 da kuma ma’aikatan lafiyar da suka sadaukar da rayukansu wajen kula da su.

Sanchez ya ce, Sarki Felipe na VI zai jagoranci bikin wanda zai samu halartar shugaban Majalisar Turai, Charles Michel da Shugabar Gudanarwa Kungiyar Ursula von der Leyen da shugaban Majalisar Dokoki David Sasoli da Babban Jami’in Diflomasiya Josep Barrol da kuma shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI