Macron ya halarci bukin cika shekaru 80 da kirar tinkarar mamayar Nazi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yarima Charle na Burtaniya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yarima Charle na Burtaniya Tolga Akmen/Pool via REUTERS

Jumma’an nan ake bukin tunawar cika shekaru 80 da jajircewar da janar Charle De Gaulle ya nuna wajen yakar ‘yan nazi a lokacin yakin duniya na biyu.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi tattaki har zuwa Birtaniya kasar da janar De Gaulle ya yi zaman mafaka, inda ya gudanar da bukin a can, tare da nuna godiya ga kasar.

Shugaba Macron ya yi amfani da wannan dama don isar da godiyar Faransa ga Birtaniya wace a cewar sa take a matsayin cibiyar Faransa mai ci gashin kan ta a zagayowar bikin cikon shekaru 80 a lokacin da Janar De Gaulle dake samun goyan bayan Churchill a wancan lokaci ya kira Faransawa da su ta shi tsaye domin yakar dakarun Jamus da suka kama birnin Paris.

Shugaba Macron a wannan ziyara ya samu ganawa da yarima Charles da maid akin sa Camilla a gidan su ,kafin daga bisani ya isa wurin da aka ajiye bututumin Sarki Georges na shida da sarauniya Elisabeth da janar De Gaulle wurin da ya ajiye furanin,bayan haka ya kuma mika lambar girma ga birnin na Landan.

Birtaniya ta taka muhimiyar rawa a a lokacin , lokacin da akasarin faransawa suka fida rai da sake samun inci kamar yada yake rubbuce a littatafai.

Yayinda yarima Charles ya gabatar da jawabin sa ,ya na mai yabawa daddadiyar hulda dake tsakanin kasashen biyu,Faransa da Birtaniya,Yarima ya jaddada cewa za su ci gaba da aiki kafada da kafada.

Bayan wannan biki shugaban Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci ofishin marigay Janar De Gaulle dake Landan,kafin ya samu ganawa da Firaministan Birtaniya Boris Johnson.

A karshe ana sa ran Emmanuel Macron da Borris Johnson za su Ambato batun annobar Coronna virus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI