EU

EU ta gabatar da yarjejeniyar farfado da arzikinta

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen REUTERS/Piroschka van de Wouw

Shugabannin Kungiyar Tarayyar sun gabatar da wata yarjejeniya mai cike da rarrabuwar kawuna kan yadda za su samar da kudaden farfado da tattalin arzikin nahiyarsu da annobar coronavirus ta yi wa mummunar illa.

Talla

Kasashen Turai na fusakantar koma-bayan tattali arziki mafi muni a tarihinsu na shekaru 63 da dungulewa, yayin da a halin yanzu suka dukufa wajen farfado da nahiyar baki dayanta bayan coronavirus ta kassara ta.

A wani taron hoton bidiyo da suka gudanar a yau Juma’a, shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von de Leyen ta gabatar da kudirin tara Euro biliyan 750 don ceto nahiyar, kuma muddin wannan kudiri ya samu karbuwa, zai kansance wani babban tarihi da aka kafa a nahiyar.

Shi kuwa shugaban Majalisar Zartaswar Kungiyar Turai kuma mai masaukin-baki, Charles Michel ya ce, suna da nauyin da ya rataya a wuyansu da ya kamata su sauke, kuma yanzu ne lokacin da ya dace a cewarsa.

Sai dai wasu kasashen Turai guda hudu da suka hada da Netherlands da Sweden da Denmark da Austria na nuna turjiya, inda suka yi alkawarin bin diddigi kan yadda za a raba da kuma kashe kudaden.

Su dai kasashen Italiya da Spain da coronavirus ta fi yi wa illa a Turai, na fatar gaggauta samar da kudaden farfado da tattalin arzikin, yayin da suka nemi agaji daga sauran kasashen da suka fi dasawa da su don ganin a hanzarta samar da kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI