Birtaniya

Birtaniya ta bayyana harin birnin Reading a matsayin na ta'addanci

Wani sashe na birnin Reading da wani mahari ya kashe mutane 3 a farmakin wuka.
Wani sashe na birnin Reading da wani mahari ya kashe mutane 3 a farmakin wuka. REUTERS/Peter Nicholls

Jami’an ‘yansandan Birtaniya sun ce mutane 3 da harin wukar birnin Reading ya ritsa da su na ci gaba da karbar kulawar gaggawa yayinda su ke tsare da maharin mai shekaru 25 wanda ya hallaka mutane 3 a farmakin kan lambun shakatawar jama’a da yammacin jiya Asabar.

Talla

‘Yan sandan Thames Valley sun ce za su tuhumi matashin da harin ta’addanci ne wanda wasu bayanai ke nuna cewa dan gudun hijira ne daya shiga kasar daga Libya, ko da dai ‘yansandan ba su gasgata batun ba.

Acewar shugaban sashen yaki da ta’addanci na ‘yansandan bayan bincike kan matashin sun gano babu wasu dalilai da suka sanya shi kaddamar da farmakin face tsagwaron ta’addanci.

Tuni dai Firaminista Boris Johnson ya aike da sakon jaje ga ilahirin al’ummar birnin na Reading mai dogon tarihi da ya kafu tun a karni na 12.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI