Faransa

Macron ya bada umarnin sake bincikar Fillon

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci sake nazari kan tuhumar da ake yi wa tsohon Firaministan kasar, Francois Fillon na biyan matarsa kudaden albashi ba tare da gudanar da aiki ba. Wannan ya biyo bayan zargin da aka yi cewar 'yan siyasa ne suka matasa wa masu gabatar da kara lamba wajen gaggauta binciken abin da ya hana Fillon tsayawa takara.

François Fillon tare da matasarsa Pénélope
François Fillon tare da matasarsa Pénélope STEPHANE DE SAKUTIN / AFP
Talla

Kafin bankado zargin amfani da ofishinsa da Francois Fillon ya yi wajen biyan matarsa albashi ba tare da gudanar da wani aiki ba, tsohon Firaministan na sahun gaba wajen lashe zaben shugaban kasar Faransa kamar yadda hasashe ya nuna.

Wannan mataki na kaddamar da bincike kan zargin ya shafi kimar Fillon wanda ya fice daga cikin takarar, kana ya gurfana a gaban kotu domin kare kansa daga wannan zargi.

Batun shari’ar ya dada tasowa a makon da ya gabata, inda tsohuwar babbar mai gabatar da kara ta shaida wa 'yan majalisun kasar cewar ta yi ta fuskantar matsin lamba wajen gaggauta gurfanar da Fillon lokacin da take rike da mukaminta.

Wannan ya sa magoya bayan Fillon suka dauki matsayin nata a matsayin shaidar da ke nuna cewar torsasa ta akayi wajen taimaka wa a bata wa tsohon Firaministan suna a shari’ar da ake sa ran yanke hukunci ranar 29 ga watan nan.

Wannan ya sa shugaba Emmanuel Macron bada umurnin sake nazarin tuhumar da ake wa Fillon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI