Macron zai ziyarci Netherland kan shirin farfado da Turai
Wallafawa ranar:
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na shirin ziyartar kasar Netherlands a gobe Talata inda zai gana da Firaminista Mark Rutte kan shirin sake farfado da tattalin arzikin Turai da kasar ke jan kafa akai.
Fadar shugaban Faransa ta ce shugaba Macron zai isa Haque ne da tsakiyar rana, inda zai ci abincin yamma tare da mai masaukin sa, kana kuma su gana da juna kan shirin da kungiyar kasashen Turai ke da shin a fardado da tattalin arziki sakamakon illar da annobar coronavirus tayi.
Shugabannin kasashen Turai na fuskantar rarrabuwar kawuna kan shirin yadda za’a raba euro biliyan 750 ga kasashen da ke yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu