Wata kwaya ta kashe daruruwan mutane a Faransa
Wallafawa ranar:
Masu shigar da kara na gwamnatin Faransa sun bukaci kotu da ta garkame shugaban wani kamfanin harhada magunguna saboda wata kwaya da ya samar da ta yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.
Kamfanin ya samar da kwayar maganin Mediator da ya ce, tana magance ciwon siga da kuma rage tiba, amma wannan magani ya haddasa asarar daruruwan rayukan jamna’a.
Maganin na Mediator ya shafe tsawon shekaru 33 a kasuwa, inda kimanin mutane miliyan 5 suka yi amfani da shi kafin a janye shi a shekarar 2009 saboda fargabar cewa, yana haifar da ciwon zuciya.
Yanzu haka dai, masu shigar da kara na gwamnatin Faransa sun bukaci a daure Jean-Phillippe Seta har tsawon shekaru biyar a gidan yari saboda rawar da ya taka a badakalar maganin Mediator, sannan kuma a ci kamfaninsa tarar Euro miliyan 8.2 saboda laifin boye bayanai dangane da illar maganin.
Seta shi ne na biyu a jerin shugabannin kamfanin harhada magunguna na Servier, yayin da ya musanta aikatata ba daidai ba, yana mai cewa, ko kadan ba shi da masaniya game da illar maganin na Mediator har sai a shekarar 2009, wato bayan kasashen Amurka da Spain da Italiya sun haramta amfani da maganin.
Kazalika, Hukumar da ke Sanya Ido kan Ingancin Magunguna ta Faransa na fuskantar tuhuma saboda gazawarta a aikinta, yayin da daya daga cikin masu shigar da karar ya bukaci a ci ta tarar Euro dubu 200.
Kimanin mutane 500 ake kyautata zaton sun mutu a sanadiyar amfani da maganin, amma kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce, watakila adadin ya karu zuwa dubu 2 da 100.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu