Faransa

Faransa ta bude Eiffel Tower duk da fargabar coronavirus

Dubban masu yawon bude daga sassan duniya ke ziyartar Hasumiyar Eiffel Tower
Dubban masu yawon bude daga sassan duniya ke ziyartar Hasumiyar Eiffel Tower REUTERS/Benoit Tessier

Faransa ta bude hasumiyar Eiffel Tower ga masu yawon bude ido a wannan Alhamis bayan ta kasance a rufe na tsawon watanni uku saboda annobar coronavirus, yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke gargadin cewa, annobar na ci gaba da kamari a nahiyar Turai.

Talla

Sake bude hasumiyar ta Effiel Tower na zuwa ne a daidai lokacin da mahukunta suka kagu a ci gaba da gudanar da harkoki kamar yadda aka saba gabanin bullar coronavirus.

Sai dai alkaluman da aka fitar a makon jiya, sun nuna cewa, nahiyar Turai na sake fuskantar barazanar karuwar masu dauke da cutar ta coronavirus kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana, tana mai gargadi cewa, tsarin kiwon lafiya a wasu kasashe ka iya shiga cikin wani yanayi na matsi.

Sai dai adadin sabbin masu dauke da cutar a Turai na da karanci idan aka kwatanta da kasashen yankin Amurka, inda a Brazail da Amurka, aka samu mutane kimanin dubu 80 da suka kamu da cutar a jiya Laraba kadai.

Wasu jihohin kasar Amurka sun fara duba yiwuwar sake maido da dokar kulle, yayin da wani kwararre a Brazil, Domingos Alves ya ce, kasarsa na tura jama’a barzaku ta hanyar sake bude tattalin arzikin kasar cikin hantsari.

Har yanzu dai, gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da fafukar samar da daidaito a fannin kiwon lafiyar al’umma domin yaki da cutar ta coronavirus wadda ta harbi kusan mutane miliyan 10 tare da lakume rayuka kusan dubu 500.

Kazalika wannan annoba ta yi raga-raga da tattalin arzikin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI