Rasha-Coronavirus

Rasha na zaben raba-gardama kan tsawita mulkin Putin

Masu zaben raba-gardama a Rasha sanye da kyallen rufe baki da hanci saboda coronavirus
Masu zaben raba-gardama a Rasha sanye da kyallen rufe baki da hanci saboda coronavirus REUTERS/Yuri Maltsev

Al’ummar Rasha na zaben raba gardama game da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, matakin da zai bai wa shugaban kasar Vladmir Putin damar zarcewa kan karagar mulki har zuwa shekara ta 2036.

Talla

Tuni jami'an tsaro suka dukufa wajen hana cinkoson jama'a a yayin zaben don hana bazuwar cutar coronavirus, yayin da zaben zai kai har zuwa ranar Laraba mai zuwa.

Mahukuntan kasar sun tanadi kyallayen rufe baki da hanci  da sabulun wanke hannu da mutane kimanin miliyan 110 za su yi amfani da su a yayin kada kuri'unsu a yankuna 10 na kasar.

Masu aikin rarraba kayayyakin zaben, su ma sun sanya safar hannu duk dai da nufin gujewa kamuwa da cutar coronavirus.

Hukumomin Rasha su zakuda da zaben ne daga 22 ga watan4 da ya gabata zuwa wannan lokaci saboda fargaban cutar coronavirus.

A watan Janairu shugaba Putin ya bullo da tsarin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kuma Majalisun Dokokin kasar ba su yi wata-wata ba wajen amincewa da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI