Hari da wuka ya hallaka mutane 3 a Scotland
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga Glasgow dake Scotland sun ce akalla mutane 3 suka mutu lokacin da wani ya dabawa mutane wuka a wani otel, yayin da jami’an tsaro suka harbe shi har lahira.
Talla
Rundunar Yan Sandan Scotland ta tababtar da cewar jami’in ta guda na daga cikin wadanda aka dabawa wukar, yayin da Yan Sanda dauke da makamai yanzu haka ke gudanar da bincike a unguwar.
Jagorar Yankin Nicola Sturgeon ta bayyana kaduwa da lamarin, yayin da Yan Sanda ke mata bayanin abinda ke faruwa akai akai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu