Turai da Amurka na fargabar sake dawowar korona
Wallafawa ranar:
Sabbin rahotanni na nuna kasar Amurka da kasashen Turai na ta daukan matakan sake shiga halin kunci sakamakon alamun sake bullar annobar cutar coronavirus a kasashen na su.
Ya zuwa yanzu dai mutane samada dubu 480 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon kamuwa da wannan cuta na Coronavirus tun fara bullar wannan cuta daga kasar China a karshen shekarar data gabata, kuma ya zuwa wannan lokaci masana na cewa a makon da zamu shiga alkaluman mutanen da suka kamu da cutar za su zarce miliyan 10 a kasashen duniya.
Manyan kasashen duniya kuma na ta duba batun sake bude harkokin tattalin arzikinsu bayan hana walwala da aka yin a tsawon wani lokaci saboda yaduwar wannan cuta.
A kasar Amurkan bayan toshe duk wata harka na tsawon watanni 2, sabbin kamuwa da wannan cuta da ake sake samu, na tada hankula da ke sa ake ganin ala tilas sai an sake daukan sabbin matakai yanzu.
Amurka daicikin kwana day arak, yau an sami sabbin kamuwa 37,667 ga kuma mace-mace da suka kai 692
Kungiyar lafiya ta duniya, WHO ta yi gargadin kasashen Turai ayi hattara domin annobar na nan zata sake kunno kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu