Kotun Faransa ta daure tsohon Franministan kasar

Tsohon Franministan Faransa Francois Fillon da mai dakinsa yayin zaman kuto a birinin Paris 29 ga watan Yuni 2020.
Tsohon Franministan Faransa Francois Fillon da mai dakinsa yayin zaman kuto a birinin Paris 29 ga watan Yuni 2020. REUTERS

Kotu a birnin Paris na kasar Faransa ta yankewa tsohon Franministan kasar François Fillon hukuncin daurin shekaru 5 da suka hada da 2 na zaman gidan yari, karkashin badakalar daukar ma’aikatan bogi, da suka hada da mai dakinsa, al’amarin da ya haifar masa da cikas a lokacin yakin zaben neman tsayawarsa takarar shugabancin kasa na shekara ta 2017.

Talla

Kotun gyaran halin dai bata ambaci ajiye mata tsohon Franministan a kurkuku a lokacin da take zartar da hukumcin ba, wanda ya hada da biyan tarar Euro dubu 375.000 tare da haramta masa tsayawa takara a cikin shekaru 10 nan gaba.

Sai kuma mai dakin ta François Fillon da abokin da ake zarginsu tare, Marc Joulaud, tsohon mataimakin takarar neman kujerar dan majalisar dokokin François Fillon a yankin Sarthe dake yammacin Faransa inda ya zama dan majalisar dokoki kotun ta zartar masu da hukumcin biyan sama da miliyan daya na Euro ga majalisar dokoki.

Ma’auratan Fillon dai sun bayyana aniyarsu ta sake daukaka kara kan hukumcin, Kamar yadda lauyarn dake karesu Antonin Lévy, da ya danganta hukumci da zama marar adalci ya sanar.

A makon da ya gabata ne dai masu kare tsohon zakaran jamíyar masu raáyin yan mazan jiya dake ci gaba da sukar binciken da aka gudanar a dai dai lokacin da ake tsakkiyar yakin neman zaben shugabancin kasar faransa na 2017, suka bukaci sake buda wata sabuwar shraá, bayan da aka gano cewa an yi amfani da matsin lamba ga kwamotin da ya gudanar da binciken da ya zargi tsohon Franministan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI