Spain ta tsare masu safarar dagwalo zuwa Afirka

Kontenoni da aka dauko kaya daga kasashen duniya
Kontenoni da aka dauko kaya daga kasashen duniya AFP/STR

Mahukuntan Spain sun tsare wasu mutane 34 da ake zargi da safarar dagwalar kayakin lantarki da na’urori masu hadari har tan dubu 2 da 500 zuwa Najeriya da wasu kasashen Afirka 7.

Talla

Binciken da aka gudanar karkashin hukumar ‘yan sanda Turai, ya gano cewar wadanda ake zargi,sunyi safarar dagwalar masu hadiri har sau 138 zuwa kasashen na Afirka tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019.

Jami’an tsaron civil Defence na kasar Spain ta kame mutanen 34 a yankunan Tenerife da tsibirin Gran Canarie na kasar Spain akasarinsu ‘yan Afrika.

Binciken ya nuna cewa kayayyakin wanda turawa ke zubar da su, kamar motoci kayayyakin amfani na gida, akwatunan Talabijin, kwanfutoti da sauransu, kimanin tan dubu 2 da 500, akayi safararsu zuwa kasashen Senegal da Ghana da Gamabia da Togo da Benin da Guinee Conakry da Saliyo sai kuma uwa uba Najeriya.

Cikin mutanen da aka tsare harda wani dan kasar Italiya mai kimanin shekaru 62, wanda ke ruwa da tsaki wajen taimakawa masu safaran da takardun kwastam, domin fitcewa da kayakin ta tekun Atlantika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI