Turai-Coronavirus

EU ta fitar da jerin kasashen da za a baiwa damar shiga Turai saboda COVID-19

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Photo: Kenzo Tribouillard/AFP

Kungiyar Kasashen Turai ta bayyana sunayen kasashe 14 da suka yarjewa al'ummominsu ziyarar nahiyar a yunkurinsu na kaucewa sake samun cutar coronavirus wadda ta yiwa kasashen nahiyar mummunar illa.

Talla

A cewar kungiyar Tarayyar Turai al'ummomin kasashen da ke da sukunin iya shiga nahiyar a yanzu sun kunshi mutanen da suka fito daga Australia ko Canada ko kuma Morocco sai 'yan Korea ta kudu.

Sauran wadanda ke da sukunin shiga kasashen nahiyar ta Turai sun kunshi mutanen Rwanda dana Japan kana al'ummar Tunisia da Uruguay.

Sanarwar kungiyar ta EU ta ce ya zuwa wannan lokaci ba za ta laminci karbar bakin da suka fito daga kasashen Amurka da Brazil da kuma China ba.

Kungiyar tace za a ci gaba da daukar 'yan kasar Birtaniya a matsayin mutanen yankin har sai an kamala tattaunawar Brexit nan da ranar 31 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI